Mujarrabi Mujarrabi

Mujarrabi

    • 4,99 €
    • 4,99 €

Description de l’éditeur

A yayin tabbatad da cikan burin nasu, bayan sunyi auren sai Allah ya yalwata dayansu da haihuwar da namiji, dayan kuwa ya jarabce ta da rashin haihuwa.

Hankalinta yayi matukar tashi a game da wannan jarabawar da Allah yayi mata, badon komai ba sai don yadda take da burin samun haihuwar ‘ya mace da kuma yadda take fuskantar barazanar kishiya daga mijinta da kuma surikarta. Mafi yawancin lokaci idan zance ya hadasu, surikar nata take musguna mata da munanan kakalai irin su "guzuma babu haihuwa, saidai aci ayi kashi".

Wannan shine dalilin da yasa ta bazama asibitoci daban-daban, domin gudanar da gwajin mahaifa. Daga karshe dai malaman asibiti sun tabbatar mata da lafiyar mahaifar ta. Don haka sai ta koma gida ta shawarci mijin nata da yaje asibiti shima yayi gwajin domin su gano mai matsalar a tsakanin su. Ashe ita bata sani ba, tun kafin ta fara yawace-yawacen asibitoci ya rigata, kuma yasan da cewar matsalar daga gareshi ne, amma duk da haka ya cigaba da mata kurari da fadar ganganci.

Da ya fahimci cewar yanzu tasan matsayinta kuma zata iya bashi matsala, sai yaci mutuncinta ya wanke zuciyarsa da borin kunya. Sannan kuma ya kara mai-maita mata kalmar “Idan kin ga da dama ki zaga dukkanin asibitocin garin nan su gwadaki ba damuwa na bane, aure ne dai sai na kara.” Ita kuma ta kudurta wa zuciyarta cewar "wallahi bazan taba tsayuwa ina gani ya kawo min kishiya cikin gidan nan ba, don wallahi idan ina ganinta zuciyata zai iya fashewa” Don haka sai tayi shawari da zuciyarta taje ta samo ciki a waje. Ta samu zaman lafiya da surukarta, kuma allah ya cika mata burinta na haihuwar ‘ya mace.

Karanta labarin 'Mujarrabi' domin jin yadda ta kaya. Zaku iya siyan bugaggiyar littafin ta Amazon ko Ebay, sannan kuma zaku iya siya musamman domin karantawa a na'ura mai kwakwalwa (waya ko kwamfuta).

GENRE
Policier et suspense
SORTIE
2014
1 février
LANGUE
EN
Anglais
LONGUEUR
69
Pages
ÉDITIONS
Hayat Alsanuzi
DÉTAILS DU FOURNISSEUR
Draft2Digital, LLC
TAILLE
115
Ko
The Mistletoe Murders: A Nietzschean Murder Mystery The Mistletoe Murders: A Nietzschean Murder Mystery
2019
The Tempest The Tempest
2019
Evert Tredoux Evert Tredoux
2020
The Blue Bell Villa The Blue Bell Villa
2018
Strange New World Strange New World
2022
Dawn Breaks Dawn Breaks
2017
Ribar Kishi Ribar Kishi
2014
Garin Gabas Garin Gabas
2014