Garin Gabas Garin Gabas

Garin Gabas

    • £2.49
    • £2.49

Publisher Description

Tafiya tayi tafiya --- mahaya sun jika --- dawaki ma sun jike; bakajin karar komai a hanyar dajin Balhare sai na sakaraftun dawaki tamkar a filin yaki. Babu zato babu tsammani domkin Boka Kuntuki dake kan gaba ya ture, boka ya kama igiyar linzami da hannu biyu ya ja har saida tabon zama suka fito a kafafun dokin na baya. Ya daga kafa ya dire sannan ya garzaya izuwa gefen wani tsohon bingi – inda ruwa ya fara kwanciya a cikin kankanin kwazazzabo.

Da ganin haka sai Jarumi Juma ya umarci dukkanin tawagarsa da su kame nasu linzamin, sannan shima ya dire cikin gaggawa ya nufin inda babban bokan ya ziyarta. Boka Kuntuki ya daga hanu sama yana sumbatu irin na tsafi kamar yadda ya saba, kafin kace 'kwabo' har hoton abinda ke faruwa a kofar kogon Babban Dodo ya bayyyana a ciki wannan ruwan da ke gabansa. Jarumi Juma ya gane wa idanusa yadda Dangus ya yayi kisan gilla wa dukkanin dakarun da ke gadin kogon. Ya kuma rike littafin kunjce dodon fuskarsa cike da jarumta, ya nufi cikin kogon kai tsaye.

Take suka yanke shawari – Jarumi Juma da tawagarsa suka juya da baya domin komawa Garin Gabas, saboda masaniyar musibar da zai auku da zarar an bude wannan dodo. Boka Kuntuki kuma ya cigaba da tafiyarsa a kan hanyar Dajin Balhare domin ceto Sarki da Sarauniya Zinnira.

GENRE
Fiction & Literature
RELEASED
2014
31 January
LANGUAGE
EN
English
LENGTH
51
Pages
PUBLISHER
Hayat Alsanuzi
SIZE
139.9
KB

More Books Like This

Rooh - Meeting Soul Rooh - Meeting Soul
2021
Haal-e-Dil Haal-e-Dil
2022
Way Back To You Way Back To You
2021
Maririlag na mga Hagod ng Brotsa Maririlag na mga Hagod ng Brotsa
2015
MAUSAM ZINDAGI KE… MAUSAM ZINDAGI KE…
2020
Paboko Paboko
2020

More Books by Hayat Alsanuzi

Mujarrabi Mujarrabi
2014
Ribar Kishi Ribar Kishi
2014